27 Oktoba 2020 - 11:12
​David Friedman: Saudiyya Ta Taimaka Wajen Kulla Hulda Tsakanin Larabawa Da Isra’ila

Jakadan Amurka a haramtacciyar kasar Isra’ila David Friedman ya bayyana cewa, gwamnatin Saudiyya ta taka gagarumar rawa wajen kulla alaka tsakanin wasu gwamnatocin larabawa da Isra’ila.

ABNA24 : A zantawarsa da jaridar Isra’ila ta The Jerusalem Times, jakadan kasar Amurka a Isra’ila David Friedman ya bayyana cewa, rawar da Saudiyya ta taka wajen jawo hankulan larabawa domin su kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila mai girma ce, kuma mai matukar muhimmanci.

Ya ci gaba da cewa, za mu yi amfani da wannan damar domin karfafa tsaron Isra’ila da kuma kare manufofinta a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda kuma wannan babbar dama ce wajen tunkarar hadarin Iran ga Amurka da Isra’ila, musamman ganin cewa UAE tana daga cikin kasashe da suke da iyaka da Iran, wadda kuma tana cikin kasashen da suka kulla alaka da Isra’ila.

Dangane da batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan kuwa, David Friedman ya bayyana cewa, a halin yanzu an dakatar da wanann shiri na wani dan lokaci, domin bayar da dama ga larabawan da suke da sha’awar kulla alaka da Isra’ila, amma daga bisani shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan zai ci gaba, kuma za a aiwatar da shi kamar yadda aka tsara.

Gwamnatocin kasashen UAE, Bahrain da kuma Sudan ne dai ya zuwa yanzu suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a bayyane, yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa akwai wasu kasashen larabawan da suke kan hanya, daga cikinsu kuwa har da Saudiyya.

342/